A yayin taron, firaminista Li Keqiang ya kuma mika sakon murna ta sabuwar shekara ga dukkanin masanan kasashen waje dake aiki a nan kasar Sin.
Haka kuma, wasu masana sun bayyana ra'ayoyi da shawarwarorinsu kan harkokin kwaskwarima a fannonin tattalin arziki da ayyukan koyarwa, da kuma kiyaye muhalli da dai sauransu.
Firaminista Li ya kuma saurari shawarwarin masanan, inda ya kuma yi musayar ra'ayoyi da su.
Li Keqiang ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta aiwatar da manufofin janyo hankulan masanan kasashen ketare, wadanda za su dace da bukatun masanan dake zuwa aiki da kuma zaman rayuwa a kasar ta Sin. Kaza lika za a ba da biza ta shiga da fita daga kasar Sin sau da dama ta tsawon shekaru biyar, da kuma ta shekaru goma, tare da samar da matakai masu sauki na samun izinin zama na dindindin a kasar Sin da dai sauransu.
Bugu da kari, firaminista Li ya ce, ana fatan masanan kasashen ketare za su ba da karin shawarwari ga kasar Sin, da kuma ba da gudummawa ta bunkasar kasar, da kyautatuwar harkokin masana'antun kasar da dai sauransu. (Maryam)