in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya yi ganawa da takwarar aikinsa ta kasar Birtaniya
2018-02-01 09:17:03 cri

A jiya Laraba ne, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwarar aikinsa ta kasar Birtaniya Theresa May, yayin ganawar shekara-shekara a tsakanin firaministocin Sin da Birtaniya.

Li Keqiang ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya tana kan gaba fiye da dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen yammacin duniya. Bisa halin da ake ciki a duniya, Sin tana mai hankali sosai kan kasar Birtaniya da ma dangantakar dake tsakaninta da kasar. Ya yi imani cewa, bunkasuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu ta dace da muradunsu, kana hakan zai taimaka ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a yankin da ma duniya gaba daya.

A nata bangare, Theresa May ta bayyana cewa, ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai Burtaniya ta bude wani muhimmin babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya. Za kuma ta yi amfani da wannan ziyara wajen kara inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a wannan lokaci mai muhimmancin gaske. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China