Jakadun kasashe mambobin Tarayyar Turai a MDD, sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa a jiya Jumma'a, inda suka bayyana rashin amincewarsu da matakin Shugaban Amurka Donald Trump, na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila. Suna masu kira da a tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Sanarwar da Jakadun Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya da Sweden suka fitar, ta ce ba sa goyon bayan matakin na Amurka da kuma fara shirin mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Kudus daga Tel Aviv. Inda suka ce matakin ya sabawa kudurorin kwamitin sulhu na MDD, kuma ba zai amfanawa yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin ba.
Sanarwar ta ce dole ne tabbatar da matsayin birnin Kudus ya kasance bisa cimma yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
A cewar jakadun, bisa ka'idojin Tarayyar Turai, matsayar mambobinta ita ce, kasancewar birnin Kudus matsayin babban birnin Isra'ila da Falasdinu. Kuma kafin sannan a wajensu, babu wata kasa dake da iko da birnin. (Fa'iza Msuatpha)