Yau Talata a nan Beijing, Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya shugabanci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin kan Shanghai wato SCO, inda ya gabatar da shawarwari 6 kan yaddaz za a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin mambobin kungiyar a sabon yanayin da ake ciki.
Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar da suka halarci taron sun yaba wa kokarin da kasar Sin take yi wajen kara inganta ayyukan kungiyar a matsayinta na shugaban kungiyar na wannan karo. Sun kuma nuna fatansu na taimakawa kasar Sin ta yadda za a samu sakamako mai kyau a yayin taron koli na Qingdao. (Tasallah Yuan)