in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNESCO ta sanya allon kashi na kasar Sin cikin kayayyakin tarihi na duniya
2017-12-26 19:38:40 cri

Mahukuntan kasar Sin sun sanar a yau Talata ce, hukumar raya Ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD ko UNESCO a takaice ta sanya wani allon kashi mai dauke da zane na kasar Sin cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya.

Mataimakin ministan Ilimi na kasar Sin kana shugaban kwamitin adana kayayyakin da suka shafi harshe na majalisar gudanarwar kasar ta Sin Du Zhanyuan, shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, kasusuwan wasu sassa ne allon kashi ko bayan kunkuru, wadanda ake amfani da su wajen yin duba a zamanin daular Shang, wato daga shekarar 1600 zuwa ta 1046 kafin haihuwar Annabi Isa.

Jami'in na kasar Sin ya ce, sigogin kasar Sin sun yi tasiri matuka a duniya, musamman kasashe makwabta, kana sun ba da gagarumar gudummawa a fannin wayewar kan dan-Adam.

Sanya wannan kashi cikin kayayyakin tarihi da hukumar ta UNESCO ta yi, ya nuna irin muhimmancin da yake da shi a duniya.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China