in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira ga mambobin kungiyar SCO su kara hada hannu a fannonin tsaro da cinikayya da hadin kan yanki
2017-12-02 12:53:28 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, su kara inganta hadin kai ta fuskar tsaro da cinikayya da kuma sufuri tsakaninsu, ta yadda za a samu dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin.

Da yake jawabi ga taron firaministocin kasashen kungiyar a birnin Sochi na Rasha, Li Keqiang ya gabatar da wani kuduri dake neman kasashen su amince da yarjejeniyar yaki da tsattsauran ra'ayi tun da wuri domin tabbatar da tsaron yankin.

Kasashe 8 mambobin kungiyar ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yayin taron da ya gudana cikin watan Yunin da ya gabata a birnin Astana na Kazakhstan, sai dai ta na bukatar samun amincewa a kasashen mambobi da suka hada da Sin da Kazakhstan da Kyrgyzstan da Rasha da Tajikistan da Uzbekistan da India da Pakistan kafin ta fara aiki.

Li keqiang, ya ce tsaro shi ne tubalin samun ci gaba, ya na mai kira da a kara hadin kai wajen tabbatar da tsaron yankin ta hanyar dabaru na bai daya da suka kunshi dukkan fannoni domin tabbatar da dorewar tsaro.

Yayin da ake samun kyautatuwar harkokin tattalin arziki da cinikayya a duniya, Firaministan na kasar Sin ya bukaci mambobin kungiyar su saukaka tare da inganta 'yancin cinikayya.

Baya ga haka, Li Keqiang ya yi kira da a gaggauta samar da hanyoyin sada kasashen, ta hanyar samar da wani tsarin fasaha da zai inganta fannin sufuri. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China