Li Keqiang ya ce, kasar Sin za ta gudanar da bikin baje-kolin kayayyakin da aka shigo da su daga ketare na kasa da kasa karo na farko a birnin Shanghai a watan Nuwambar badi, wannan wani muhimmin mataki ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka don saukaka harkokin cinikayya da kuma kara bude kofarta ga kasashen waje. Li yana fatan bangarori daban-daban za su goyi-bayan wannan mataki.(Murtala Zhang)