in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNESCO ta bayyana rashin jin dadi game da shirin Isra'ila na janyewa daga hukumar
2017-12-30 12:40:37 cri

Darakta Janar ta hukumar UNESCO mai bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD dake da mazauni a birnin Paris Audrey Azoulay, ta bayyana rashin jin dadi game da matakin Isra'ila na janyewa daga hukumar, tana mai bayyana bukatar tattaunawa don cike gibin dake akwai tsakanin mambobin hukumar.

Wata sanarwa da Audrey Azoulay ta fitar a jiya Jumma'a, ta ce a matsayinta na Darakta Janar ta UNESCO, Gwamnatin Isra'ila ta sanar da ita jiya, game da matakinta na janyewa daga hukumar daga ranar 31 ga watan Disamban 2018, matakin da aka sanar tun ranar 12 ga watan Oktoban da ya gabata.

Ta ce Isra'ila ta kasance mamba a hukumar tun cikin shekarar 1949, kuma ta damu ainun da janyewar, tana mai cewa la'akari da ikon da UNESCO ke da shi, a ganinta abun da ya fi dacewa shi ne, kasashe su shawo kan bambance-bambancen dake tsakaninsu a cikin hukumar, amma ba a waje ba.

Ta ce yayin da ake samun takaddama tsakanin kasashe mambobi, shi ga cikin ayyukan hukumar ka'in da na'in, zai bada dama ta tattaunawa da hadin kai da ake bukata.

A ranar 12 ga watan Oktoban da ya gabata ne Amurka ta sanar da UNESCO cewa, za ta janye daga hukumar a ranar 31 ga watan Disamban 2018. A kuma ranar ce Isra'ila ta yi maraba da matakin, inda ita ma ta ce za ta duba iyuwar daukar makamancin matakin saboda mayar da ita saniyar ware da hukumar ke yi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China