An sanya biranen kasar Sin hudu cikin jerin birane masu kirkire-kirkire na duniya
2017-11-01 15:38:37
cri
Hukumar UNESCO a jiya Talata ta bayar da sanarwa, inda ta sanya birane hudu na kasar Sin da suka hada da Changsha, da Macao, da Qingdao da kuma Wuhan, cikin jerin birane masu kirkire-kirkire na duniya, don nuna muhimmancin kirkire-kirkire a wajen tabbatar da dauwamammen ci gaban birane.
Ban da haka, an kuma sanyan birane 9 na Afirka a cikin wannan jadawali.(Lubabatu)