in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya tsawaita wa'adin aikin MONUSCO
2018-03-28 10:18:21 cri
Jiya Talata, kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani kudurin bai daya, inda aka tsawaita wa'adin aikin dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Kongo wato MONUSCO a takaice na tsawon shekara guda, wato zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2019.

Wannan kudurin ya tabbatar da muhimmin aikin na MONUSCO, wato wajen kiyaye fararen hula, da kuma tabbatar da yarjejeniyar siyasa da bangarori daban daban na kasar Kongo Kinshasa suka cimma a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2017 da dai sauransu.

Baya ga haka, kudurin ya taimakawa MONUSCO wajen fatattakar dakaru masu dauke da makamai na kasar, ta hanyar kai dauki daga dakarun soji, kana da sa ido, da bada rahoto kan yanayin take hakkin bil Adama da na saba dokar jin kai ta kasa da kasa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China