in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar OPCW ta isa Syria
2018-04-22 16:41:54 cri
Kungiyar haramta amfani da makamai masu guba wato OPCW ta ce, tawagar bincike da ta aike zuwa Syria ta riga ta isa garin Duma a jiya Asabar, domin gudanar da bincike kan hare-haren makamai masu guba da aka zargin an kai garin.

Cikin rahoton da ta fitar, Kungiyar ta ce za ta gabatar da rahoto ga dukkanin kasashen da suka kulla yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba, da zarar ta samu sakamako bisa nazarin da za ta yi kan bayanan da tawagar binciken za ta samo. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China