in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Siriya na son hada kai da kungiyar haramta amfani da makamai masu guba don gudanar da bincike
2018-04-17 10:59:28 cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya, Faisal Mekdad, ya ce, gwamnatin kasar na da niyyar hada kai da kungiyar haramta amfani da makamai masu guba ta duniya wato OPCW a takaice, domin gudanar da bincike kan zargin da ake wa kasar na kai hari ta hanyar amfani da makamai masu guba, kana, Siriya za ta samar da duk abun da OPCW ke bukata a yayin aikinta.

Kamfanin dillancin labaran Siriya wato SANA ya ruwaito Mekdad yana cewa, bisa goron gayyatar da gwamnatin kasar ta ba ta, tawagar kungiyar OPCW ta riga ta isa birnin Damascus kwanaki ukun da suka gabata, inda ta yi shawarwari da gwamnatin Siriya, tare da tattaunawa kan yadda za su gudanar da bincike cikin adalci ba tare da rufa-rufa ba. Mista Mekdad bai ce uffan ba game da yadda tawagar ke gudanar da ayyukanta.

A kwanakin baya ne, wato a ranar 7 ga wata, aka kai wani hari yankin Ghouta dake gabashin birnin Damascus na kasar Siriya, abun da wasu ke zargin cewa, harin na makamai masu guba ne. Daga baya a daren ranar 13 ga wata, agogon Amurka, Amurkar da Faransa da Birtaniya suka kai hari kan sansanonin soja dake Siriya, abun da ya janyo ce-ce-ku-ce daga wasu kasashen duniya game da halalcinsa, inda suka yi kira da a gudanar da bincike kan zargin da ake wa Siriya na amfani da makamai masu guba don kai hari cikin adalci.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China