Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, an kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa dasu magance tsananta yanayin da ake ciki, da warware batun ta hanyar yin shawarwari bisa dokokin kasa da kasa.
Ma Zhaoxu ya yi nuni da cewa, a ganin kasar Sin, ya kamata a yi bincike kan batun kai harin makamai masu guba a kasar Syria, da gabatar da sakamakon bincike mai gaskiya. Kafin hakan, bangarori daban daban basu yi hasashen sakamakon ba. Hanyar siyasa ita ce hanya daya kawai da za'a bi wajen warware batun Syria, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa dasu ci gaba da nuna goyon baya ga MDD data shiga-tsakani, da yin kokarin warware batun Syria ta hanyar siyasa tare. (Zainab)