in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya kasa zartas da daftarin kudurin adawa da kai harin soja ga kasar Syria
2018-04-15 17:19:52 cri

Kwamitin sulhun MDD ya gaza zartas da daftarin kudurin adawa da kai harin soja ga kasar Syria da kasar Rasha ta gabatar a ranar 14 ga wata.

Daftarin ya yi Allah wadai da kasar Amurka da kasashe kawayenta saboda sabawa dokokin kasa da kasa da dokokin MDD da kai hari ga kasar Syria, ya bukace su dasu dakatar da kai hari a kasar Syria don magance cigaba da sabawa dokokin kasa da kasa da tsarin mulkin MDD da yin amfani da karfin tuwo.

A wannan rana, membobi 3 a cikin dukkan membobin kwamitin sulhun 15 sun amince da daftarin, guda 8 sun ki amincewa da shi, kuma guda 4 sun janye daga jefa kuri'un. Don haka an kasa zartas da daftarin.

Bayan hakan, zaunannen wakilin Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya yi bayani cewa, Sin ta ki amincewa da yin amfani da karfin tuwo wajen daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da girmama ikon mallakar kasa da kasa da 'yancin kansu da hadin kan kasa, da cikakken yankin kasa da kasa. Duk aikin sojan da ya sabawa ka'idojin tsarin mulkin MDD da kwamitin sulhun ya sabawa dokokin kasa da kasa da ka'idojin kula da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kara kawo illa wajen warware matsalar kasar Syria. Bisa wannan matsayi, kasar Sin ta nuna amincewa ga daftarin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China