Shugabannin sun yi kiran ne yayin taron koli na kawancen kasashen Larabawa na yini daya da aka yi jiya Lahadi a birnin Zahran dake gabashin Saudiyya.
Wata sanarwar da taron ya fitar ta ce, kasashen sun lura da matakan da kasashen yamma ke dauka a kasar Syria. Kuma sun yi Allah wadai da amfani da makamai masu guba kan jama'ar kasar. Sanarwar ta kuma nanata muhimmancin warware matsalar Syria a siyasance, kana ta yi kira ga duk sojojin kasashen waje dake Syria da su janye daga kasar, don kiyaye ikon mulkin kai da cikakken yankunan kasar Syria. (Bilkisu Xin)