Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ce ta bayyana haka, yayin da take amsa tambayoyin 'yan jaridu dangane da luguden wuta kan kasar Siriya da Amurka da Birtaniya da kuma Faransa suka yi da sanyin safiyar yau Asabar
Madam Hua ta kuma jaddada cewa, kasar Sin tana ganin cewa, ya kamata a gudanar da bincike daga dukkan fannoni bisa hanya madaidaiciya, kan zargin da ake wa Siriya na amfani da makamai masu guba, ta yadda za'a samu sakamako mai tushe. Sin ta ce, ya kamata kasashe daban-daban su ci gaba da goyon-bayan MDD wajen shiga-tsakani kan rikicin Siriya.(Murtala Zhang)