in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Siriya ta yi tir da harin da wasu kasashe suka kai mata
2018-04-14 17:36:44 cri
Gwamnatin kasar Siriya gami da sojojinta sun yi tir da harin da wasu kasashe, ciki har da Amurka, suka kai mata da safiyar yau Asabar, inda suka jaddada cewa, matakan da Amurka da sauran wasu kasashe suka dauka sun saba wa dokokin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya.

Ma'aikatar harkokin wajen Siriya ta fitar da wata sanarwa a yau, inda ta ce, gwamnatin kasar ta yi Allah wadai da harin makamai masu linzami da Amurka da Birtaniya da Faransa suka kai mata, abun dake nuna cewa, wadannan kasashe na bijirewa dokokin kasa da kasa, kana, abun da suka yi, zai tsananta halin da ake ciki a duk fadin duniya, da kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniyar.

Ita ma rundunar sojan Siriya ta fitar da wata sanarwar dake cewa, da sanyin safiyar yau, Amurka da Birtaniya gami da Faransa sun yi kutse cikin Siriya, har sun harba wasu makamai masu linzami kimanin 110 kan birnin Damascus da dai sauran wasu sassan kasar. Sanarwar ta ce sojojin Siriya sun kakkabo akasarin makaman.

Har wa yau, sanarwar ta ce, irin wadannan hare-hare ba za su sanyaya gwiwar sojojin Siriya gami da kawancensu ba, wajen ci gaba da ayyukansu na murkushe 'yan ta'adda a kasar. Haka zalika, ba zai kawo tsaiko wajen ci gaba da kare ikon mallakar kasar da kuma kare jama'arta ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China