Ma Zhaoxu ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, yanayin da ake ciki a Syria na matukar hadari, wanda ya ce yana kan wata gaba mai muhimmaci na zabi tsakanin zaman lafiya da yaki.
Ya ce a wannan lokaci da al'amura suka tsananta, ya kamata kwamitin sulhun ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, na gina hadin kai da cimma matsaya tare da yin abun da ya kamata domin hana barkewar yaki.
Ya ce a ko da yaushe, kasar Sin ta fi mayar da hankali kan hawa teburin sulhu wajen warware rikici, inda kuma ta kasance mai adawa da amfani da karfi ko yin barazanar amfani da karfi a harkokin kasa da kasa.
Jami'in na kasar Sin ya ce yin gaban kai wajen daukar matakan soji ta hanyar kaucewa kwamitin, ya saba da dokoki da manufofin kwamitin da kuma dokokin da ka'idojin kasa da kasa.
Ya ce ya kamata a girmama cikakken ikon da Syria ke da shi da ikon kasancewarta matsayin kasa daya dunkulalliya mai cin gashin kanta. (Fa'iza Mustapha)