in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka ya sanar da daukar matakan soja a kan Syria
2018-04-14 10:53:08 cri

A jiya da dare ne shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa, ya umurci sojojin kasar tare da hadin kan sojojin Burtaniya da Faransa, su dauki matakan soja kan na'urorin sojin Syria, a wani matakin mayar da martani kan harin makamai masu guba da aka kai yankin Ghouta ta gabas da ke gabashin kasar Syria.

Rahotanni sun ce, a ranar 7 ga wata ne aka kai harin makamai masu guba a yankin Ghouta ta gabas, inda a jiya, gwamnatin Amurka ta ce ta samu abubuwan da za su iya shaidar harin, ta na mai zargin gwamnatin Rasha da rashin daukar wani mataki kan batun. Sai dai gwamnatin Syria ta yi watsi da wannan zargi na Amurka.

Gidan talabijin na Syria, ya ruwaito a yau Asabar cewa, kasashen da suka hada da Amurka da Faransa da Birtaniya, sun dauki matakan soji kan Damascus, babban birnin kasar da sanyin safiyar yau. Rahoton ya kara da cewa, sojojin kasar na mai da martani ga harin bisa tsarinsu na kare kasar daga sararin sama, tsarin da ya zuwa yanzu, ya kakkabo makamai masu linzami 13. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China