Wata sanarwa da Sakatare Janar din ya fitar jiya ta ruwaito shi ya na cewa, ya na bibiyar rahotonnin hare- hare ta sama da Amurka da Birtaniya da Faransa suka kai Syria. Ya ce akwai wani nauyi, musammam yayin da ake batun zaman lafiya da tsaro, na yin biyayya ga dokokin MDD da ma na kasa da kasa.
Ya bukaci kasashe mambobin Majalisar su yi hangen nesa a wannan yanayi mai cike da hadari tare da kaucewa yin abubuwan da ka iya tsananta halin da ake ciki da kuma wahalhalun al'ummar Syria. (Fa'iza Mustapha)