Cikin sanarwar ya ce, ya buga waya ga zaunannun wakilan kasashe 5 na MDDr domin jaddada damuwarsa matuka kan yanayin da kasar Syria ke ciki a halin yanzu, inda ya kuma jaddada bukatar daukar matakan magance tabarbarewar yanayi a kasar.
Haka kuma, ya ce, labarin da aka fitar game da kaddamar da hare-haren makamai masu guba a kasar Syria ya bata masa rai kwarai da gaske, kana yana bakin ciki sakamakon kasa cimma matsaya guda kan wannan batu a kwamitin sulhu na MDDr. Ya ce, babban burinsu shi ne fitar da al'ummomin kasar Syria daga mawuyacin hali. (Maryam)