in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Rasha da Faransa sun tattauna batun Syria ta wayar tarho
2018-04-07 13:08:06 cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya tattauna da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron kan batun Syria da kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwa, yayin zantawar da suka yi jiya ta wayar tarho.

Wata sanarwa da fadar Kremlin ta kasar Rasha ta fitar a jiya, ta ce, bisa gayyatar da Faransa ta yi masa, shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna da Shugaba Emmanuel Macron, a kan halin da kasar Syria take ciki a halin yanzu, inda Mr. Putin ya yi bayani game da sakamakon da aka cimma yayin ganawar da ya yi da shugabannin kasashen Turkiya da Iran kan batun Syria, a ranar 4 ga wata a babban birnin Ankara na Turkiya.

Shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, ya kamata a warware batun Syria ta hanyar siyasa bisa shawarar da aka yanke yayin cikakken zaman taron tattauna batun na Syria da aka yi a birnin Sochi na Rasha, haka kuma, ya kamata a gaggauta kafa kwamitin kundin tsarin mulkin kasa ta Syria a birnin Geneva.

Bugu da kari, tattaunawar shugabannin biyu ta mayar da hannkali kan ayyukan janye dakaru 'yan adawa da gwamnatin kasar Syria da al'ummomin kasar daga yankin Ghouta ta Gabas na kasar, inda shugaba Putin ya jaddada cewa, bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD, ya kamata gamayyar kasa da kasa su hada hannu domin samar da taimakon jin kai ga al'ummomin kasar Syria baki daya.

Haka zalika, shugabannin biyu sun cimma ra'ayi daya kan ci gaba da shawarwarin yadda za a warware rikicin Syria. Ban da haka kuma, sun tattauna kan manyan batutuwan da suka shafi dangantakar dake tsakaninsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China