Cikin sanarwar, an kuma bayyana cewa, shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin za su halarci kwamitin kolin hadin gwiwar kasashen Turkiya da Rasha da za a yi a ranar 3 ga wata. Ban da haka kuma, shugabannin biyu za su halarci bikin aza harsashi na tashar nukiliya ta samar da wutar lantarki ta farko ta kasar Turkiya watau tashar Akkuyu da za a yi a wannan rana.
A ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 2017, shugabannin kasashen Turkiya, Rasha da Iran sun yi ganawa a birnin Sochi na kasar Rasha, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan ci gaban yanayin da ake ciki game da batun kasar Syria da kuma hanyoyin warware matsalar da abin ya shafa da dai sauransu, sa'an nan sun fidda wata sanarwa cikin hadin gwiwa, yayin da suka yi kira da a gudanar da cikakken zaman taron neman sulhu kan kasar Syria.
Daga bisani kuma, a ranar 30 ga watan Janairu, an yi cikakken zaman taron yin shawarwari kan batun kasar Syria a birnin Sochi, inda bangarori daban daban suka fidda wata sanarwa cikin hadin gwiwa, yayin tsaida kuduri kan kafa kwamitin kundin tsarin mulkin kasar ta Syria. (Maryam)