in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
kashin farko na 'yan tawaye sun mika wuya a gabashin Ghouta a lokacin da ake tsaka da kai kayakin jin kai
2018-03-10 13:37:19 cri

Kashin farko na 'yan tawaye sun ajiye makamai a yankin gabashin Ghouta dake gabas da Damascus babban birnin Syria, inda suka koma yankin dake karkashin ikon gwamnati a daidai lokacin da motocin kayayyakin agaji suka shiga yankin a jiya Jumma'a domin kai kayayyakin jin kai da zai wadatar da mutane 12,000.

A cewar gidan talabijin na kasar, jimilar 'yan tawaye 13 ne suka isa zauren bada agaji na yankin Wafidin dake arewa maso gabashin Damascus, bayan sun fito daga lardin Douma.

Sai dai aka tantance 'yan tawayen kafin su shiga motar da za ta kai su wani wuri da ba a sani ba.

Duk da yanayin da ake ciki na wahalar isa yankin, motocin bada agaji na MDD sun isa yankin Douma dake gabashin Ghouta a jiya Jumma'a.

Kakakin kungiyar bada agaji ta duniya Inji Sedky, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, manyan motoci 13 dauke da kayayyakin agaji ne suka shiga Douma, inda ta ce kayayyakin da motocin suka sauke sun hada da kunshin abinci 2,400 da buhunan garin alkama 3,240 wadanda za su wadatar da mutane 12,000. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China