Jami'in ya bayyana a gun taron kwamitin sulhun MDD kan batun jin kai na kasar Syria da aka gudanar a wannan rana cewa, Sin ta yi kokarin samar da gudummawa ga jama'ar kasar Syria. A watan da ya gabata, Sin ta kara samar da gudummawar ruwa da abinci da hidimar kiwon lafiya da wurin kwana da sauransu ga jama'ar kasar Syria da suka rasa gidajensu ta kafar kwamitin Red Cross na duniya. Kasar ta ki amincewa ga duk irin aiki na kai hari ga fararen hula, ya kamata a magance tsananta irin halin da ake ciki a kasar.
Ya kara da cewa, a ranar 24 ga watan Febrairu, bangarori daban daban na kwamitin sulhun MDD sun zartas da kuduri mai lamba 2401, ta haka an tabbatar da hadin kan kwamitin sulhun, da samar da dama ga tsagaita bude wuta da dakatar da rikice-rikice a kasar Syria.
Ma Zhaoxu ya ce, Sin ta kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi kokari tare da gudanar da ayyukansu don tabbatar da aiwatar da kuduri mai lamba 2401 yadda ya kamata. (Zainab)