in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria ta musanta amfani da makamai masu guba a gabashin Ghouta
2018-04-09 13:54:36 cri
Kafar yada labarai ta kasar Syria ta ba da labari a jiya Lahadi 8 ga wata cewa, gwamnatin Syria ta musanta yin amfani da makamai masu guba a gabashin yankin Ghouta dake Damascus, kuma ta ce zargin da aka yi mata babu kamshin gaskiya.

Wannan kafar ta ruwaito maganar wani jami'in gwamnati dake cewa, da zarar gwamnatin ta cimma nasara wajen murkushe ta'addanci, sai a dinga zargin ta da laifin yin amfani da makamai masu guba, ya tabbatar da cewa, irin wannan zargi ya samarwa 'yan ta'addanci hujja ta maido da karfinsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China