Ya ce, ko wace kasa tana bukatar kudade da farko yayin da take kokarin raya tattalin arziki da masana'antunta. Idan babu kudi, zai yi wuya ga kasashen Afirka su cimma burin raya masana'antu da zamanintar da kasashensu.
Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan batun basusukan da kasashen Afirka suke karba. Sin na daukar ra'ayin samun bunkasuwa tare, da gina muhimman kayayyakin more rayuwa da su taimaka wajen raya sana'o'in kasashen Afirka, da cin gajiyar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da inganta karfin kasashen Afirka na samun bunkasuwa mai dorewa da kansu, da taimakawa kasashen Afirka wajen magance karuwar basusukan da ake binsu. (Zainab)