in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan za a saurari ainihin burin jama'ar nahiyar Afirka
2018-03-16 19:49:34 cri

Yau Jumma'a ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, a shekarun baya, kasashen Sin da Djibouti sun samu sakamako mai kyau a bangaren hadin gwiwa ta fannoni daban daban, lamarin da ya kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri na a-zo-a-gani, kana ya ba da muhimmiyar gudummawa, wajen samun zaman lafiya da ci gaba a yankin.

Sai dai a cewarsa, wasu daga kasar Amurka masu mugun nufi sun yi kalami kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Djibouti. Game da hakan, kasar Sin na fatan za su saurari ainihin burin jama'ar Afirka. Lu Kang ya kuma yi nuni da cewa, Sin tana maraba da sauran kasashen duniya, da su shiga cikin aikin raya tattalin arzikin Afirka, a kokarin kara azama kan ci gaba da wadatar nahiyar. Sa'an nan kuma, kasar Sin na fatan za a mai da hankali kan ba da gudummawa tare wajen samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali da wadata a nahiyar Afirka, a maimakon sauran fannoni.

An labarta cewa, a kwanan baya, ministan kudi na Djibouti ya ce, gwamnatin Djibouti na maraba da kasar Sin, wajen kara shiga aikin gina tashar jiragen ruwa a kasar. Ya ce Djibouti ba ta fuskantar barazana ta fuskar moriya a manyan tsare-tsare, kamar yadda wasu daga Amurka suke bayyana damuwar hakan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China