Yau ne Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kasar Sin ba ta goyi bayan duk wani nau'i na nuna wariyar al'umma. Don haka duk ya yi amfani da wata dama domin ya takali huldar da ke tsakanin kasahen Sin da Afirka, ba zai yi nasara ba.
Geng Shuang ya bayyana haka ne yau a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, domin mayar da martani ga rahotanni da wasu kafofin yada labaru na kasashen duniya suka watsa, inda suke zargin cewa, wani gajeren wasan kwaikwayo da aka nuna a yayin murnar bikin bazara na shekarar 2018 yana da nasaba da batun nuna wariyar launin fata. (Tasallah Yuan)