Yana mai cewa, an kafa cibiyoyin raya fasahohin ayyukan gona a kasashen Afirka guda 14, inda Sin ta tura masana da dama zuwa kasashen. Haka kuma, Sin ta gayyaci masana da jami'an hukumomin ayyukan gona na kasashen Afirka zuwa nan kasar Sin domin kara samun kwarewa kan wasu fasahohin zamani.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma samar da taimako ga wasu kasashen Afirka a fannonin na'urorin ayyukan gona na zamani da maganin kashe kwari masu barnata amfanin gona da dai sauransu. (Maryam)