Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama yana ganin cewa, kasar Sin tana yaki da cin hanci da karbar rashawa ba tare da nuna sassauci ko kadan ba, ta kuma gurfanar da wadanda suka taba aiwatar da wannan laifi a gaban kuliya, lamarin da ya kasance abin koyi ga dukkan kasashen Afirka.
Haka kuma, ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohamed ta nuna cewa, kasashen Afirka da kasar Sin za su iya yin hadin gwiwa kan aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa, ta yadda za a kafa al'adu na yaki da cin hanci da karbar rashawa a kasashen Afirka, haka kuma, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kan wannan aiki zai taimaka matuka wajen kyautata kwarewar kasashen Afirka game da aikin yaki da rashawa .
An kira taron kolin kungiyar AU a hedkwatar kungiyar ne dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha tun daga ranar 22 zuwa ranar 29 ga watan nan da muke ciki, kuma babban taken taro na wannan karo shi ne, "Cimma nasarar yaki da cin hanci da karbar rashawa, domin neman dauwamammen ci gaba a fannin yin kwaskwarima a kasashen Afirka". (Maryam)