Jiya Alhamis 1 ga watan Maris, Staffan de Mistura, wakilin musamman na MDD mai kula da batun Sham ya bayyana a yayin taron manema labaru a birnin Geneva cewa, MDD za ta ci gaba da kara azama kan warware batun na Sham a siyasance, ya kuma jaddada cewa, ya kamata a hanzarta aiwatar da kudurin MDD mai lamba 2401 daga dukkan fannoni, da tsagaita bude wuta a Sham, a kokarin kawo karshen wahalhalu da kunce da yake-yake suka haddasawa wa fararen hula. (Tasallah Yuan)