Cikin wata gajeriyar sanarwar da rundunar sojin ta fitar, ta ce 'yan tawayen dake gabashin Ghouta, sun samu umarnin yin amfani da makamai masu guba a yankin domin yi wa sojojin gwamnati sharri.
Rahotanni na cewa, 'yan tawayen za su yi amfani da sinadarai masu guba a kusa da iyakarsu da sojojin Gwamnati, inda za su kai hari kan fararen hula, ta yadda kasashen Birtaniya da Amurka da sauran kasashen Turai za su zargi dakarun Syria da kai harin. (Fa'iza Mustapha)