Bayan da aka sanar da sunan Julius Maada Bio, dan takarar jam'iyyar adawa mafi girma a kasar Saliyo wato jam'iyyar SLPP, a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasar, Mr. Maada Bio ya sha rantsuwar kama aiki a daren 4 ga wata a birnin Freetown, fadar mulkin kasar. (Tasallah Yuan)