Sakamakon zaben shugaban kasar ta Saliyo ya nuna cewa, Maada Bio ya samu kuri'u kimanin kashi 51.81 bisa 100, yayin da abokin karawarsa, Samura Kamara, na jam'iyya mai mulkin kasar wato APC ya samu kashi 48.19 bisa 100 na yawan kuriun da aka kada. (Ahmad Fagam)