in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Saliyo ta ce ta shiryawa zaben kasar na yau Laraba
2018-03-07 10:33:22 cri
Al'ummar Saliyo kimanin miliyan 3 da suka yi registar zabe ne ake sa ran za su kada kuri'a a zaben yau Laraba. Zaben da masu sanya ido suka bayyana a matsayin muhimmi ga kasar dake yammacin Afrika.

Jami'iyyun siyasa 16, ciki har da jam'iyya mai mulki ta All People's Congress APC da babbar jam'iyyar adawa ta Sierra Leone People's party SLPP ne suka shiga zaben.

Daraktan sashen yada labarai da wayar da kai na hukumar zaben kasar Albert Massaquoi, ya ce hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zaben na yau, inda ya ce an riga an tura kayakin zabe zuwa yawancin sassan kasar.

A cewar shugabar hukumar NEW, mai sa ido kan harkokin zabe ta kasar, Maercella Samba-Sesay, sun tura jami'an sa ido 11,122 wadanda za su sa ido a dukkanin rumfunan zaben dake daukacin lardunan 16 na kasar.

Hukumar NEW ita ce babbar mai aikin sanya ido kan zabukan kasar, inda ta kunshi kungiyoyin al'umma dake bibiyar zabuka a kasar tun daga lokacin yi wa masu zabe rejista har zuwa lokacin kidaya kuri'u. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China