in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar PLA ta kammala aikin da na'urar bibiyar kwayoyin cuta masu yaduwa a kasar Saliyo
2017-09-09 13:40:57 cri

Ayarin jami'an lafiya na sojojin 'yantar da al'umma na kasar Sin wato PLA, ya kammala aiki da na'urar bibiyar cututtuka masu yaduwa a Saliyo.

A karshen watan Augusta ne shugaban kwalejin kimiyyar aikin lafiya na rundunar Zhang Shitao, ya ce aikin ya gudana cikin shekara guda ba tare da matsala ba, yana mai cewa lokacin fargaba ya wuce.

La'akari da tasoshin bibiyar cututtuka 22 da rundunar sojin Saliyo ta kafa, tun fara aikin cikin watan Augustan da ya gabata, na'urar ta kula da marasa lafiya sama da 8,000 inda ta bibiyi sama da cutuka 30 da alamomin cutuka 40.

Jami'in ya ce kai tsaye, na'urar na ba Saliyo damar bibiyar cututtuka da samun gargadi a kan kari, haka zalika ta na taimakawa kasar Sin wajen tunkarar cututtuka masu yaduwa da za a iya shiga da su kasar da kuma batutuwan da suka shafi lafiyar al'ummomin kasashen waje.

Tun daga watan Yunin 2016 rundunar PLA ta tura ayarin jami'an lafiya guda biyu zuwa Saliyo, inda suka horas da sojojin kasar tare da aiki da su kan na'urar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China