in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da babban zabe a Saliyo
2018-03-08 10:04:03 cri
Jiya Laraba, aka jefa kuri'u a babban zaben kasar Saliyo, inda ake zabar sabon shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin kasar guda 132.

Gaba daya akwai jam'iyyu guda 16 da suka halarci zabe na wannan karo, inda 'yan takara guda biyu da suka hada da, dan takarar jam'iyyar mai mulkin kasa ta APC Samura Kamara, da dan takarar jam'iyyar adawa ta SLPP Julius Maada Bio, suke neman hawa kan ragamar mulkin kasar.

Bisa dokokin kasar ta Saliyo, idan ba'a samu wanda ya lashe samar da kashi 55 bisa dari na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar ba, to za a zabi 'yan takara guda biyu da suka fi samun kuri'u don su shiga zaben a zagaye na biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China