in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben kasar Saliyo ta dage zaben shugaban kasar
2018-03-27 09:23:47 cri
Hukumar zaben kasar Saliyo (NEC) ta fidda wata sanarwa a jiya Litinin inda ta bayyana cewa, ta dage gudanar da zaben shugaban kasar wanda ta shirya gudanarwa a ranar 27 ga wannan wata inda ta mayar da shi zuwa ranar 31 ga watan na Maris.

NEC ta ce, ta dauki wannan matakin dage ranar zaben ne sakamakon jinkirin da ta samu game da samar da kayayyakin aiki a sanadiyyar umarnin babbar kotun kasar na sanya takunkumin gudanar da zaben a ranar Asabar. Sai dai kotun ta dage takunkumin ne a ranar Litinin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China