Dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar APC mai mulkin kasar shi ne ke kan gaba da kashi 44.6 bisa 100, sai kuma dan takarar babban jam'iyyar adawar kasar SPP wanda ke bi masa baya da kashi 42 bisa 100. Yayin da dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar NGC yake a matsayi na 3 da kashi 6.6 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.
A cewar shugaban hukumar ta NEC, a halin yanzu, kashi 25 bisa 100 na sakamakon zaben ne aka sanar, kuma ba shi ne cikakken sakamakon zaben ba.
Ya kara da cewa, a nan gaba za su sanar da kashi 50 bisa 100 na sakamakon zaben kafin karshen wannan rana ta yau.
Sama da mutane miliyan 3 ne suka kada kuri'unsu a zaben inda aka jefa kuri'un domin zabar sabon shugaban kasa da 'yan majisar dokokin kasar da na majalisun kananan hukumomi tun a ranar 7 ga watan Maris. (Ahmad Fagam)