Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Rasha Igor Konashenkov, ya bayyana jiya Laraba cewa, ana bukatar daukar matakan jin kai na gaggawa a yankin kasar Syria dake karkashin mallakar kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Rasha na TASS ya ruwaito Konashenkov na cewa, yanayin rayuwa ya ta'azzara sosai a yankunan Ar-Raqqah da Al-Tanf na kasar Syria, wadanda ke hannun kawancen yaki da ta'addanci na duniya a karkashin jagorancin Amurka, don haka ana bukatar kasashe daban daban su samar da taimakon jin kai cikin gaggawa. A ciki, dakaru sun yi garkuwa da 'yan gudun hijira kimanin dubu 60 a yankin Al-Tanf. (Kande Gao)