in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe na yin kwaskwarima don bude kofa ga waje, in ji shugaban kasar
2018-04-01 13:24:40 cri
Kwanan baya, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa wanda zai kawo ziyarar aiki a kasar Sin tsakanin ranakun 2 da 6 ga watan Afrilu ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Zimbabwe tana yin kwaskwarima a fannin bude kofa ga waje, da nufin janyo hankulan masu zuba jari, ta yadda za ta sami damar raya tattalin arzikinta. A yayin da kasar take gudanar da wannan kwaskwarima, ta yi koyi daga kasar Sin kan fasahohin kasar wajen neman ci gaba, kuma kasar Zimbabwe tana maraba da zuwan masu zuba jari daga kasar ta Sin.

Haka kuma, a yayin da yake tsokaci kan shirin "Ziri daya da Hanya daya", ya bayyana cewa, tabbas ne shirin zai karfafa mu'amalar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma kawo sauki ga ciniki dake tsakanin kasa da kasa, ba wanda zai ki shiga cikin shirin, kuma a ko da yaushe kasarsa ta Zimbabwe zai nuna goyon baya ne kan shirin.

Game da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da za a yi a watan Satumba na shekarar bana kuwa, shugaba Mnangagwa ya bayyana cewa, ya riga ya sami takardar gayyata, kuma zai halarci dandalin da za a yi a birnin Beijing. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China