Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, sabuwar Jam'iyyar ta New Patriotic Front wato NPF, ta sanar da nada Ambrose Mutinhiri a matsayin shugaban Jam'iyyar kuma 'dan takarar shugaban kasa a zaben.
Ambrose Mutinhiri wanda tsohon Brigedier Janar ne kuma dan gwagwarmayar neman 'yancin kasar, ya yi murabus daga Jam'iyyar ZANU PF da majalisar dokokin kasar ne a ranar Juma'ar da ta gabata, domin nuna adawarsa da abun da ya kira 'sabawa kundin tsarin mulki wajen cire Shugaba Mugabe'.
Shugaban na sabuwar Jam'iyyar NPF, ya taba rike mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaba Mugabe.
Robert Mugabe dai ya yi murabus ne a watan Nuwamban bara, bayan ya fuskanci matsin lamba daga sojoji, inda aka maye gurbinsa da Emmerson Mnangagwa da ya sauke daga mukamin mataimakin shugaban kasa makonni biyu kafin ya yi murabus, sanadiyyar rikicin da ake a jam'iyyar game da wanda zai maye gurbin shugaban kasar. (Fa'iza Mustapha)