in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan makamashin Zimbabwe ya yabawa kasar Sin bisa samar da kudaden aikin fadada lantarkin kasar
2018-03-28 09:49:20 cri
Ministan makamashin kasar Zimbabwean Simon Khaya Moyo, ya yabawa kasar Sin sakamakon samar da kudaden gudanar da aikin fadada tashar samar da lantarki ta ruwa a kasar mai karfin megawati 300.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Xinhua a Kariba, gabanin kaddamar da shirin fadada aikin samar da lantarkin wanda shugaban kasar Zimbabwean Emmerson Mnangagwa zai kaddamar a yau Laraba, ministan ya bayyana cewa, aikin zai taimakawa kasar wajen takaita kudaden da kasar ke kashewa wajen sayen lantarki daga kasashen waje.

Kamfanin samar da lantarki na Sinohydro na kasar Sin ne ya gudanar da aikin fadada lantarkin na tashar samar da lantarki ta Kariba inda ya samar karin megawati 150 daga shekarar 2014 a kan kudi dalar Amurka miliyan 535.

Ana saran idan aikin ya kammala za'a daga matsayin lantarkin kasar daga megawati 750MW zuwa karfin megawati 1,050 MW, wanda shine zai kasance aikin tashar samar da lantarki mafi girma a kasar Zimbabwe yayin da ake son zarta adadin lantarkin da tashar samar da lantarki ta Hwange ke sawarwa wanda yakai megawati 900.

Kasar Zimbabwe tana bukatar lantarki mai karfin megawati 1,400 MW, amma tana iya samar da megawati 900 ne na lantarkin, lamarin da ya tilasta mata nemo ragowar daga ketare.

Minista Moyo ya ce, Zimbabwe tana fata kasar Sin za ta ci gaba da taimaka mata wajen bunkasa fannin lantarkinta domin ta cimma nasarar samar da adadin lantarkin da kasar ke bukata, kasancewar kasar tana fuskantar samun karuwar masu zuba jari tun bayan zuwa sabuwar gwamnatin shugaban kasar karkashin jagorancin Mnangagwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China