in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta koma kungiyar kasashe renon Ingila a bana
2018-02-05 09:42:51 cri

Jaridar "The Sunday Mail" ta kasar Zimbabwe ta labarta a ranar 4 ga wata cewa, a bana Zimbabwe za ta koma kungiyar kasashe renon Ingila. Tuni kuma shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar ya riga ya sanar wa gwamnatin Ingila matsayin kasarsa.

Wannan shi ne karo na farko da kafofin yada labaru suka watsa labaru dangane da ajandar Zimbabwe ta komawa kungiyar kasashe renon Ingila.

An labarta cewa, shugaba Mnangagwa ya bayyana matsayin kasarsa na shirin komawa kungiyar kasashe renon Ingila a fili ne, yayin da yake yin shawarwari da Harriet Baldwin, wakilin musamman na gwamnatin Ingila kuma sabon ministan harkokin Afirka na Ingila, wanda ke ziyara a Zimbabwe.

An ruwaito kalaman jami'an Zimbabwe da suka halarci shawarwarin suna cewa, shugaba Mnangagwa ya bayyana wa bangaren Ingila burinsa na mayar da kasar sa kungiyar kasashe renon Ingila. Amma ya jaddada matsayin Zimbabwe kan batun yin gyare-gyare ga harkokin gonaki, inda ya ce, ba ja da baya game da gyare-gyaren. Ya ce kamata ya yi Ingila ta dauki nauyin biyan diyya ga masu gonaki fararen fata.

A shekarar 2002 da ta gabata ne kwamitin kungiyar kasashe renon Ingila, ya dakatar da Zimbabwe daga kasancewa mamban kungiyar har tsawon shekara guda, saboda yana ganin cewa, an yi magudi a babban zaben da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2002. A watan Disamban shekarar 2003, a yayin taron kolin kungiyar kasashe renon Ingila da aka yi kuma, kwamitin ya tsai da kudurin ci gaba da dakatar da Zimbabwe daga kungiyar, daga baya kuma Zimbabwe ta sanar da janyewa daga kungiyar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China