in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta taimakawa Zimbabwe a zabukan da za ta shirya a wannan shekara
2018-02-21 12:24:45 cri
Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka(AU) Moussa Faki Mahamat, ya bayyana aniyar kungiyar na taimakawa kasar Zimbabwe na ganin ta shirya zabuka masu tsafta a tsakiyar wannan shekara.

Faki ya bayyana hakan ne jiya Talata yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka kira da ministan harkokin wajen kasar ta Zimbabwe Sibusiso Moyo bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki uku da ya kai kasar ta Zimbabwe. Ya ce, wata tawagar kungiyar za ta zo kasar inda za ta hada kai da hukumar da shirya zabukan ya rataya a wuyanta

Mahamat ya kuma yaba da yadda aka mika mulki a kasar cikin ruwa sanyi. Ya ce, a wani bangare na nauyin dake kanta, kungiyar AU za ta taimakawa gwamnatin rikon kwaryar kasar da kayan aiki don tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Ya ce, ya gamsu da wannan ziyara da kuma tattaunawar da suka yi da ma matakan da mahukuntan Zimbabwe suka dauka na bude kofofinsu na siyasa da tsarin demokiradiya don tabbatar da cewa, an gudanar da zabuka cikin adalci wadanda za su samu karbuwa a kasar.

A nasa jawabin ministan harkokin wajen kasar Zimbabwe Sibusiso Mayo ya bayyana cewa, shugaban hukumar zartaswar AU ya lura da cewa, gudanar da zabuka masu adalci cikin nasara, zai taimaka wajen kawo karshen yadda aka mayar da kasar saniyar ware da sake dawo da taimakon da kasashen duniya ke baiwa kasar.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce dai tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya sauka daga mulki, bayan da sojojin kasar suka shiga tsakani, kana shugaba Emmerson Mnangagwa ya maye gurbinsa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China