A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, Lu Kang ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Zimbabwe, tana kuma fatan kokari tare da kasar Zimbabwe, wajen inganta dangantakar dake tsakaninsu don amfanin kasashen biyu da jama'arsu.
An gama aikin fadada tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa dake kudancin gabar Kariba, wadda kasar Sin ta tattara kudin aiwatarwa a kasar ta Zimbabwe. Lu Kang ya bayyana cewa, bayan kammala aikin, za a fadada samar da wutar lantarki, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Zimbabwe, kuma Sin na farin ciki matuka game da hakan.
Ya ce akwai irin wadannan ayyuka da dama na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wanda hakan ke shaida cewa, hadin gwiwa da zuba jari da kasar Sin ta yi a kasashen Afirka, sun taimakawa kasashen nahiyar wajen samar da kayayyaki, da samun moriyar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, wadanda kuma gwamnatocin kasashen Afirka da jama'arsu ke maraba da su. (Zainab)