in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mata ne suka mamaye kaso mafi yawa na masu rejistar zabe a Zimbabwe
2018-03-02 10:15:32 cri
Hukumar Zaben kasar Zimbabwe, ta ce mata ne suka mamaye kaso mafi yawa na wadanda suka yi rejistar zaben dake karatowa, wanda aka shirya gudanarwa a tsakiyar shekarar nan.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, Kwamishinar hukumar Joyce Kazemba, ta ce kididdigar wucin gadi da aka yi, ta nuna cewa mata ne suka mamaye kaso 54.5 na masu rejistar zabe, inda ta ce akalla mutane miliyan 5.3 ne suke da rejistar zabe a kasar.

Joyce Kazemba ta ce jimilar musu kada kuri'a miliyan 5.1 ne aka tantance ya zuwa ranar 22 ga watan Febrerun da ya gabata, a daidai lokacin da hukumar ke kokarin samar da jerin sunayen masu kada kuri'a na wucin gadi ya zuwa farkon watan Afrilu.

Ta ce wadanda suka yi rejista da shekarunsu ke tsakanin 18 da 34 sun kai kashi 43.5 na jimilar, yayin da masu shekaru 60 zuwa sama suka mamaye kaso 13.6.

Fadar mulkin kasar wato Harare, shi ne ke da mafi yawan wadanda suka yi rejista da adadin ya kai kashi 44.4, inda mahaifar shugaban kasar Emmerson Mnangagwa wato lardin Midlands ke rufa masa baya da kaso 38.8. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China