in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yabawa Sin kan gudummawar da ta bayar na warware batun zirin Koriya
2018-03-30 13:35:51 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yaba matuka da kasar Sin, bisa gudummawar da ta bayar wajen warware batun zirin Koriya, yana mai cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen warware batun.

Mr. Guterres ya bayyana haka ne a jiya, a hedkwatar MDD dake birnin New York, inda ya ce ya yi farin ciki kwarai, dangane da ziyarar aiki da shugaban kasar Koriya ta Arewa ya kawo kasar Sin, domin kasar Sin kasa ce dake ba da muhimmiyar gudummawa wajen warware batun zirin Koriya. Ya kuma kara da cewa, tabbas ne ganawar da shugabannin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu za su yi ta samar da damammaki masu kyau wajen warware babban kalubalen da ake fuskanta.

Ban da haka kuma, shi ma mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da harkokin siyasa Jeffrey Feldman wanda zai kammala wa'adin aikinsa a karshen watan nan da muke ciki ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka mihimmiyar rawa kan batun warware matsalar zirin Koriya.

Shugaban jam'iyyar kwadago ta Koriya ta Arewa, kuma shugaban majalisar kula da harkokin kasa Kim Jung Un ya kawo ziyara kasar Sin ba a hukumance ba, a tsakanin ranakun 25 da 28 ga watan Maris, inda shugabannin kasashen biyu suka tattauna kan batun sassauta yanayin zirin Koriya da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China