Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Talata yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawarta wajen ganin an warware batun nukiliyar zirin Koriya, karfafa gwiwar sassa daban daban da su tattauna a tsakanin juna domin samun sakamako mai kyau, a kokarin tabbatar da samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ganin an kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya.
A jiya ne, Chung Eui-yong, wakilin musamman na shugaban kasar Koriya ta Kudu ya ziyarci kasar Sin, inda ya tattauna da bangaren Sin dangane da ziyarar da ya kai a kasashen Koriya ta Arewa da Amurka. (Tasallah Yuan)